Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Majalisa Sun Buƙaci Gwamnatin Tarayya ta Dakatar da Shirin Ƙidaya 2021

Yan majalisar wakilai sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ɗage kidayar jama’a da gidaje data shirya yi a shekarar 2021, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Wannan kiran yazo ne bayan zauren majalisar ya karɓi kudirin ƙasa wanda ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Bosso/Paikoro a majalisar wakilai ta ƙasa daga jihar Neja, Shehu Beji, ya gabatar mata a zaman ta na yau Laraba.

Yayin da yake gabatar da kudirin, ɗan majalisar yace, akwai dalilai da dama da zasu sa a dakatar da shirin kidayar waɗanda zasu shafi sakamakon da za’a samu bayan an kammala.

Ya ƙara da cewa samun nasarar wannan aikin na ƙidaya zai samu tasgaro sosai saboda matsalar tsaron da yan Najeriya ke ciki a sassa daban-daban na ƙasar nan.

“Kodai wasu an tilasta musu barin matsugunin su ko kuma an kassara musu rayuwarsu ta yau da kullum.” inji shi.

Sannan kuma Baji ya bayyana cewa babu tabbas ɗin masu ƙidayar zasu samu ingantaccen tsaro a mafi yawancin sassan ƙasar nan da matsalar tsaro ta shafa.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *