Da Allah Na Dogara, Babu Abin Da Nake Tsoron Ya Sameni, A Cewar Gwamna Zulum.

Da Allah Na Dogara, Babu Abin Da Nake Tsoron Ya Sameni, Inji Gwamnan Jihar Borno Farfesa Zulum.

Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umaru Zulum ya ce babu abin da zai sami mutum sai abin da Allah ya kaddara masa.

Gwmnan ya ce “na sha tsallake masifu kala-kala, dan haka bana tsoron komai, saboda ya kamata ace musulmi ya zama mai imani da kaddara”.

Gwamna Zulum yace burin suu shine nemawa al’ummar jihar Borno mafita, da kuma tabbatar ingantaccen tsaro a jihar, Inji Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno.

Ko a kwanakin baya ma sai da gwamnan ya tsallake rijiya da baya a wani hari da aka kai masa a kan hanyarsa ta zuwa garin Baga, wanda yayi sanadin rasuwar wasu mutane daga cikin ayarinsa wasu kuma suka jikkata.

Daga Bappah Haruna Bajoga.

Leave a Reply

Your email address will not be published.