Labarai
Da Dumi Dumi: Buhari Zai Ziyarci Kasar Ingila Domin duba lafiyarsa A Yau

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Najeriya zuwa birnin Landan na kasar Birtaniya a yau domin duba lafiyarsa.
Buhari zai tafi Landan ne bayan ya halarci taron da aka yi da manyan jami’an ‘yan sanda a Owerri, babban birnin jihar Imo.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina, a wata sanarwa a ranar Litinin, ya ce Buhari zai dawo kasar ne a mako na biyu na watan Nuwamba, 2022.
Wannan dai ba shi ne karon farko da shugaban zai tafi birnin Landan domin duba lafiyarsa ba a shekarar 2022. Buhari ya tafi kasar Ingila ne a watan Maris da Yuli domin duba lafiyarsa.