Labarai

Da ‘dumi ‘dumi: ‘Dan Majalisar tarayya daya 1 tare da ‘yan majalisar Jiha mutunGoma 10 sun koma jam’iyar NNPP ta kwankwaso mai kayan marmari.

Spread the love

Rahotonni daga jihar kano na Cewa A jiya ranar Juma’a 6 ga Mayun da muke ciki ne Mambobin Majalisar dokokin jihar Kano na
jami’iyyar PDP 10 suka sauya sheka zuwa jam’iyar NNPP ta kwankwaso mai alamar kayan marmari.

Tinda fari dai mambobin majalisar 9 ne suka fitar da sanarwar ficewa daga jami’iyyar zuwa NNPP.

‘Yan majalisar dokokin na Kano sun mika takardar fitar su ne ga shugaban majalisar Hamisu Ibrahim Chidari.

Sulaiman Yusuf Babangida Dawo-Dawo wai wakiltar Gwale shima ya bi sahun mambobin da suka sanar da ficewarsu.

Jumulla Mambobi 10 da suka sauya shekarar daga PDP zuwa NNPP sun hada da….

1.Rt Hon. Isyaku Ali Danja da ke wakiltar karamar hukumar Gezawa.

2.Hon. Umar Musa Gama mai wakiltar Nassarawa.

  1. Hon Aminu Sa’adu Ungogo daga Ungogo.
  2. Hon Lawan Hussain Chediyar ‘Yan Gurasa Dala.
  3. Hon. Tukur Muhd Fagge.
  4. Hon.Mu’azzam El-Yakub, Dawakin Kudu.

7..Hon. Garba Shehu Fammar Kubiya.

8.. Hon. Abubakar Uba Galadima Bebeji.

  1. Hon Mudassir Ibrahim Zawaciki, Kumbotso.

10- Hon Sulaiman Babangida Dawo-Dawo, Gwale.

Sanarwar hakan na zuwa ne bayan da Daraktan yada labarai na majalisar Uba Abdullahi ya fitar kuma aka rabawa manama labarai a makon daya gabata.

A gefe guda Kuma an Hango Hon Tijjani Abdulqadir Jobe Dan Majalisar tarayya Mai wakiltar Rimin Gado, Tofa da dawakin tofa a gidan Sanata Rabi’u Musa wanda ake Zargin ya Koma jam’iyar NNPP sakamakon Rashin nasarar da suka samu a kotun koli jiya a rikincin da suke da Gwamnan jihar kano kan batun Shugabancin jam’iya.

Jam’iyar NNPP ta kwankwaso na cigaba da samun karbuwa ga jama’a musamman a arewacin nageriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button