
Gwamnatin jihar Sokoto ta Aminu Waziri Tambuwa ta sace tare da karkatar da kimanin Naira biliyan 189 daga asusun gwamnati ga wasu mutane masu zaman kansu, kamar yadda takardar da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) da Babban Bankin Najeriya (CBN) ta bayyana.
Zargin na zuwa ne a daidai lokacin da Tambuwal ke shirin kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasarsa na shekarar 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Takardar mai dauke da sa hannun DCE AS Abubakar ta kuma aika wa shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa ta yi zargin cewa an bankado wasu asusun Yan kasuwa wanda ke da alaka da asusun Gwamnatin Jihar sokoto daga ranar 1 ga watan Janairun 2015 zuwa 31 ga Agusta, 2021.
A cewar Abubakar, asusun ya samu jimillar kudaden da suka kai N567,160,024,619.93 a cikin wannan lokacin inda aka karkatar da N189,155,043,825.09 ba bisa ka’ida ba.
“Kwanan nan ma’aikatar ta aiwatar da bayanan kudi na Gwamnatin Jihar Sakkwato. An yi wannan bayanin ne da nufin gano asusun gwamnatin jihar da mai yiwuwa an bankado su wajen karkatar da kudaden jama’a da kuma na jami’an gwamnati suka yi.” Inji wani bangare na takardun da Sahara Reporters ta ruwaito.
“Binciken ayyukan gwamnatin jihar daga ranar 1 ga watan Janairu, 2015 zuwa 31 ga watan Agusta, 2021, ya bankado yadda ake gudanar da mu’amalar da ba a saba gani ba a asusu kamar haka. 1) Akanta Janar Sokoto FAAC Account Number 0697434238, Access Bank.
“ii) Sakataren Gwamnatin Jiha Account Number 0700669798, Access Bank. iii) Babban Sakatare na Gwamnatin Tarayya Account Number 0700669554, Access Bank.
“3) Musamman wadannan asusu na sama sun samu jimillar kudaden da suka kai 567,160,024,619.93 (Biliyan Dari Biyar da Sittin da Bakwai, Miliyan Dari da Sittin, Dubu Ashirin da Hudu, Dari Shida da Sha Tara, Naira Tasa’in da Uku, Kobo 15, 5, 9.3) (Biliyan dari da tamanin da tara, miliyan dari daya da hamsin da biyar, naira arba’in da uku da dari takwas da ashirin da biyar, kobo tara) aka cire wa jami’an gwamnati, daidaikun mutane (wanda ake zargin masu kudi ne), kamfanoni da sauran kungiyoyi. / hukumomi.”