
An yankewa Sanata Peter Nwaoboshi, dan majalisar dattawa mai wakiltar yankin Delta ta arewa hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari bisa samunsa da laifin karkatar da kudade.
Sashen kotun daukaka kara na Legas ta yanke wa Sanatan hukuncin a ranar Juma’a.
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta gurfanar da Nwaoboshi da kamfanonin sa guda biyu – Golden Touch Construction Project Ltd da Suiming Electrical Ltd a 2018 a gaban Mohammed Idris, alkali wanda daga baya aka daukaka kara zuwa kotun daukaka kara.
Daga nan aka sake gurfanar da su a gaban Chukwujekwu Aneke a ranar 5 ga Oktoba, 2018.
A tuhume-tuhume biyu mai lamba FHC/L/117C/18, EFCC ta yi zargin cewa wadanda ake tuhumar sun karkatar da naira miliyan 322 tsakanin watan Mayu zuwa Yunin 2014.
Sai dai a wani hukunci da ya yanke a watan Yunin 2021, Aneke ya ce hukumar ta gaza tabbatar da abubuwan da suka shafi laifukan da ta tuhumi Sanatan.
Alkalin ya kuma ce karar da masu shigar da kara ta ruguje saboda “ba a kira jami’an banki don ba da shaida ba”.
Aneke ya kuma sallami kamfanonin a bisa wannan dalilin.
Ba a gamsu da hukuncin ba, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta daukaka da kara.
Da take yanke hukunci a ranar Juma’a, kotun daukaka kara ta soke hukuncin da karamar kotun ta yanke tare da yankewa Sanatan hukunci.
A cewar sanarwar da EFCC ta fitar, kotun daukaka kara ta ce alkalin kotun ya yi watsi da tuhumar da ake yi wa wadanda ake kara.
Sanarwar ta kara da cewa, “Masu gabatar da kara sun tabbatar da laifin kuma saboda haka sun samu wadanda ake tuhuma da laifi.”
Kotun daukaka kara ta kuma bayar da umarnin a raunata kamfanonin biyu.