Da dumi Dumi Kungiyar ta’addancin Boko Haram sun Kai Hari a Garin Geidam.

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin‘ yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari a garin Geidam da ke Yobe.

An tattaro cewa maharan a cikin motoci takwas dauke da makamai sun mamaye garin da misalin karfe 6 na yamma.

Wani mazaunin garin wanda ya yi magana da wakilinmu ta wayar tarho ya ce, “ayarin motocinsu ya miƙe kai tsaye zuwa inda makarantar firamaren Kafela take yayin da suka fara harbin Kai Mai uwa da wabi.

“A yanzu haka muna cikin gida muna addu’ar neman lafiyarmu, abin da zan iya fada kenan yanzu”

Kakakin rundunar ‘yan sanda Dungus Abdulkarim ya tabbatar da harin inda ya kara da cewa tuni Rundunar sojan sama suna Geidam din suna bayar da agajin gaggawa.

Bamu da Cikakken labarin wa”‘yanda Suka samu rauni ko Rasa Rai Kan Lamarin.

0 thoughts on “Da dumi Dumi Kungiyar ta’addancin Boko Haram sun Kai Hari a Garin Geidam.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *