Labarai

Da ‘dumi ‘dumi Majalisar wakilai ta amince da kudrin Uba sani na kafa asibitin cibiyar Lafiya dake Rigarsa.

Spread the love

Majalisar wakilai ta amince da kafa asibitin cibiyar Lafiya a Kaduna Sanata Uba sani ne ya gabatar kudrin a gaban majalisar, Kuma Sanatan ne ya Sanar da amincewar ta majalisar a wata sanarwarsa, Sanatan yace A yau ne ‘yan majalisar wakilai suka kada kuri’ar amincewa da kudirin kafa cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Rigasa a jihar Kaduna wannan kuduri nawa yanzu haka ya samu amincewa daga Majalisar Dattawa da ta Wakilai, yanzu dokar tana jiran amincewar shugaban kasa.

Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya dake Rigasa, idan aka kafa, za ta yi ayyuka kamar haka:

a) Za’a Samar da kayan aiki, kulawa da sarrafa Cibiyar da
samar da wuraren bincike da rigakafi da gyara sashin tiyata magani a lokacin jiyya.

b) Tallafawa da Samar da kyakkyawan muhalli da
horar da likitoci na ma’aikatar kamar yadda hukumar zata iya la’akari da tabbatar da Hakan.

c) Domin gudanar da ayyuka masu inganci kuma masu tsada ga ‘yan Najeriya.

d) Yin bita da sabunta binciken likita da bincike lokaci zuwa lokaci.

Sanatan ya kare da cewa ina son mika godiya ta musamman ga Shugaban Majalisar Dattawa, Dakta Ahmad Lawan, Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, manyan takwarorina da Honourable members bisa goyon bayansu. Sun nuna kishin Najeriya na gaskiya a hanya da kuma yadda suka tashi tare da goyon bayan kudirin.
Muna godiya a gare su tabbas.

Sanata Uba sani wanda ya ke da Kudrori ashirin 20 a gaban majalisar wanda yanzu haka wasu daga cikin sun sami amincewa tare da SA hannun Shugaban kasar Nageriya Muhammadu Buhari wanda a halin yanzu sun zama Doka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button