Labarai

Da dumi-dumi: Mutane uku sun mutu yayin wata fashewar da ta afku a jihar Kogi gabanin ziyarar Buhari

Spread the love

Mutane uku ne suka mutu sakamakon fashewar wani abu a yankin Okene da ke jihar Kogi.

Gidan Talabijin na Channels ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da safiyar Alhamis a fadar Oyinoyi da ke karamar hukumar Okenne a jihar.

Wannan na zuwa ne sa’o’i kadan kafin isowar shugaban kasa Muhammadu Buhari domin kaddamar da wasu ayyuka a jihar ta Arewa ta tsakiya.

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, jami’an ‘yan sanda na sashin yaki da bama-bamai na can a wurin da lamarin ya faru.

Sai dai babu tabbas ko fashewar ta kasance sakamakon tashin bam ne ko kuma hari aka kai wa shugaban kasar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button