Da dumi dumi Shugaba Buhari ya karbi rigakafin CoronaVirus.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi maganin rigakafin CoronaVirus na AstraZeneca, kwana daya bayan Gwamnatin Tarayya ta fara aikin allurar a kasar.

Ya karbi maganin ne a yau ranar Asabar a sabon dakin taro na Banquet na fadar shugaban kasa da ke Abuja, babban birnin kasar.

Babban likitan ya bayar da maganin ne a gaban Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, da wasu mambobin Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC).

Jim kaɗan bayan Shugaba Buhari ya ɗauki maganin, Farfesa Osinbajo shi ma ya karɓi rigakafin wanda shi ma babban likitansa ya ba shi.
Daga baya shugabanin biyu sun samu katin dauke da bayanan allurar rigakafin su ta hannun Babban Daraktan Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko (NPHCDA), Dr Faisal Shuaib.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *