Labarai

DA ‘DUMI ‘DUMI: Wasika daga Ofishin Ministan Shari’a ta wanke DCP Abba Kyari ~Cewar Kungiyar CAC.

Spread the love

Wata kungiya mai suna Citizens Advocacy Centre, CAC, ta bayyana a ranar Larabar jiya da ta gabata cewa sabanin wasu rahotannin da wasu kafafen yada labarai ke yadawa, babu wani muggan Laifi da aka samu kan DCP Abba Kyari a duk bayan an kammala bincike.

Kungiyar ta bayyana matsayar ta ne a kan wasikar karshe da ta fito daga ofishin ma’aikatar shari’a da kuma babban lauyan gwamnatin tarayya Abubakar Malami SAN, inda ta ce wasikar ta fito ta nuna karara a kan cewa duk binciken da aka yi ya wanke DCP Kyari daga dukkan zarge-zargen aikata manya-manyan laifuka wanda ya ha’da da Laifin aikata cin hanci da rashawa.

Kungiyar ta ce wasikar daga babban Lauyan kasar ta ce babu wani sisin kwabo na kudi da Hushpuppi ya ba Kyari ko kuma wani wanda ake tuhuma a Amurka kamar yadda aka yi farfaganda a lokacin fitar da batun ga manema labarai a shekarar data gabata.

A cewar kungiyar, babu wani shedu na musamman da suka bayyana a kan wani tsayayyen jami’in da ke da matsayi irin na Kyari

Kungiyar a cikin wata sanarwa da shugaban ta, Barr Joseph Donald, ya fitar, ta yi karin haske kan cewa ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, bai taba cewa tuni Najeriya ta fara tattaunawa da takwararta Amurka domin mika Kyari ba.

A cewar sanarwar, “Abin da mai girma Ministan ya ce, idan akwai wani laifi da aka samu a cikin binciken, Hakan yana iya sawa a fara shirin mika shi Kuma gashi ba a same shi da ko wanne Laifi ba Bisa Binciken kungiyar.

Ya cire shakku. Har ila yau, Ministan yana sane da cewa tsarin mika mutun zuwa Wata kasa abu ne Mai matukar wahala kuma yana da wuyar gaske ba abu ne na kai tsaye ba saboda akwai tsarin shari’ar kotu, wanda yawanci ke yanke hukunci don sanin ko akwai wani laifi da aka aikata kuma akwai isassun shaidu kan laifuka da ke tabbatar da fitar da Mai Laifi Kai tsaye ko Kuma oda anan kotun gida ta Najeriya.

A binciken farko bai haifar da komai ba face share sunan DCP Abba Kyari daga aikata muggan Laifi. Amma duk da haka, saboda matsin lamba daga wasu sassan, an sake yin wani bincike.

“Bincike na biyu ya kuma wanke Kyari a kan duk wani laifin cin hanci da rashawa amma ya tabbata daga binciken farko da bincike na biyu cewa, an ambaci wasu muhimman abubuwa guda biyu da suka shafi aikin ‘yan sanda a kan Kyari. Na daya, amfani da kafafen sada zumunta wajen kare kansa da kansa ba tare da izinin Shugaban Hukumar’yan Sanda IGP ba, na biyu, Ya kuma fara aikin binciken wani Al’amari da aka ruwaito ba tare da bin ka’idar samun amincewar koke daga IGP ba.

“Wadannan laifuffuka ana daukarsu laifin ladabtarwa ne da suka shafi harkokin ‘yan sanda na cikin gida ba cin hanci da rashawa ko wasu manyan laifuka ba. Wadannan laifuffukan da ba na cikin gama garin laifuka ba ana gudanar da su ne a cikin gida tsakanin hukumar ‘yan sanda bisa ka’idojin ladabtarwa.”

A cewar kungiyar, wasikar AGF ta fito fili ta wanke Kyari daga duk wani laifi. Maimakon haka, an tuhume shi da laifin keta ayyukan ‘yan sanda na cikin gida don haka ba za a iya mika shi ga Amurka ba.

Kungiyar ta ce ta tsaya kafada da kafada da Kyari tare da lura da cewa “Babu wani dan Najeriya da za a tursasa shi ko kuma a tuhume shi da laifin aikata wani laifi daga manyan kasashen duniya kuma a bar shi a mika shi.

“Za mu ba da goyon baya Bisa kan tsarin doka ga Kyari idan an buƙata.”

Kungiyar na cewa, “Tabbas Kyari ya taka mahimman rawa a lokacin da yake gudanar da aikinsa shiyasa mutane masu mahimmanci da tasiri suna jin cewa wannan lokaci ne da ya dace da za su biya Abba Kyari, kan karewa da kuma bauta wa ƙasarsa.

“Abin takaici, ‘yan Najeriyar da ke shiga cikin damuwa suna takurawa game da Kyari har’ila yau sune mutanen da ke kuka saboda karuwar satar mutane da garkuwa da mutane, aikata laifuka da kuma hare-haren ‘yan bindiga a fadin kasar.”

Kungiyar ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi amfani da matsayin kyakykyawan ofishinsa ya mayar da Kyari zuwa ga ofishinsa domin kawo karshen karuwae rashin tsaro a kasar tare da mayar da kasar yadda ta kasance kafin dakatar da shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button