Da dumi dumi: Wasu yan bindiga sun kashe Shugaban Hukumar shirya jarraba ta kasa(NECO) reshen jihar Niger

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba a daren Litinin sun mamaye gidan Farfesa Godswill Obioma, sukayi mishi kisan gilla kamar yadda matarsa ​​ke zargin. 

“Masu kisan sun shigo sun kashe shi sun tafi ba tare da daukar komai ba,” in ji Elizabeth Obioma ga ‘yan rahoto ta wayar tarho a safiyar ranar Talata. 

Cikin kuka sosai, Mrs Obioma ta ce mijinta ya dawo Minna ne daga tafiyar da yayi zuwa Abuja a lokacin da ‘yan bindigar suka yi mishi dirar Mikiya a gidansa suka shake shi.

An rawaito cewa Mista Obioma na fuskantar kalubale don son tsige shi daga mukaminsa na shugaban fitacciyar hukumar jarabawa na gwamnatin Najeriya ke gudanarwa.

An nada Obioma, mai shekara 67, a matsayin shugaban NECO da kyar shekara guda da ta gabata a ranar 14 ga Mayu, 2020. Ya fito ne daga Abia a yankin Kudu-Maso-Gabas da Ibo suka fi rinjaye.

Wannan lamari mai cike da bakin ciki ya faru ne kwana daya bayan da aka kashe Ahmed Gulak, wani babban dan siyasa na jam’iyyar APC mai mulki.

Cikakkun bayanai jim kadan…

Daga Maryam Ango

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *