Da dumi dumi: Yan bindiga sun dauke wasu dalibai a lokacin da suka kai hari a wata jami’a mai zaman kanta a jihar Kaduna a ranar litinin ashiringa watan afrilu.


An samu rahoto cewamakarantar mai suna Green Field University tana nan a wurin hanyar Kaduna-Abuka, a karamar hukumar Chikin ta jahar.

Wannan jami’ar itace jami’a ta farko mai zaman kanta a jahar Kaduana wadda aka kafa shekaru uku da suka wuce.

An samu labari cewa yan bindigar sun budewa mazauna wurin wuta suka sami nasarar kora su daga wurin sannan suka shiga suka sace daliban.
Kwamishinan tsaro na cikin gida, Samuel Aruwan ne ya tabbatar da aukuwar wannan lamarin ga tasoshin talabijin.

Tashoshin talabijin din sun bayyana cewar wadan da suka ga wannan al’amari a zahiri sunce yan bindigar sun shigo cikin jami’ar ne kai tsaye a ina suka bude wuta suna ta harbe harbe ta ko ina kafin suyi gaba da wasu dalibai na makarantar.

Maryam Gidado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *