Da dumi-dumi: Yan bindiga sun kashe limamin Katolika, kuma sun sace wani a Katsina

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe wani limamin katolika, Rev. Fr. Alphonsus Bello, yayinda suka yi garkuwa da wani, Rev. Fr. Joe Keke a cocin St. Vincent Ferrer Catholic Church Malunfashi, jihar Katsina, jaridar Vanguard ta ruwaito.

An tattaro cewa yan bindigan, a daren ranar Alhamis, sun afkawa cocin Katolika sannan suka fara harbi ba kakkautawa a iska, lamarin da ya jikkata wasu mutane.

Daraktan sadarwa na Sakatariyar Katolika ta Najeriya, Padre Mike Umoh, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce wadanda ake zargin sun jefar da gawar Fr Alphonsus Bello a cikin gonar da ke bayan Makarantar Horarwa ta Catechetical, Malunfashi yayin da har yanzu ba a san inda Fr. Joe Keke yake ba.

Ya ce, “A daren jiya, wasu’ yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun far wa daya daga cikin cocin Diocese na Sokoto – St. Vincent Ferrer Catholic Church Malunfashi, da ke jihar Katsina.

“An sace wasu limamai biyu, Frs. Joe Keke da Alphonsus Bello. Fr Keke, tsohon limamin Ikklesiya, yana cikin kusan shekaru 70 yayin da Fr. Bello, limamin Ikklesiya na yanzu, bai wuce shekaru 30 ba.

“A safiyar yau (Juma’a) an tsinci gawar Fr Alphonsus Bello babu rai a gonar da ke bayan Makarantar Horarwa ta Catechetical, Malunfashi.

Sai dai kuma, har yanzu ba a san inda Fr. Joe Keke yake ba. Ba a tuntube mu ba kawo yanzu.” Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa tuni mutane suka taru a gaban cocin domin nuna alhini kan lamarin.

A halin yanzu, wata majiya mai tushe daga cocin Katolika ta Sakkwato ta ce marigayin ya kasance dan kungiyar Archdiocese na Kaduna, amma yana tare da na Sokoto kuma an tura shi zuwa cocin Malumfashi da ke Katsina.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *