Da dumi Dumi ‘yan Bindiga sun kashe mutun Sha daya 11 a Karamar hukumar Safana ta Jihar katsina.

Akalla mutane 11 ‘yan fashi suka kashe yayin da wasu uku suka samu raunuka a garin Tsatskiya na karamar Hukumar Safana da ke Jihar Katsina a ranar Asabar, kamar yadda majiyarmu ta tattara.

Mutane ukun da suka jikkata na karbar kulawa a babban asibitin Dutsin-Ma.
Majiyar ta tattaro cewa maharan sun mamaye garin da misalin karfe 9:30 na safe.

An yi imanin cewa suna kan aikin ramuwar gayya ne sakamakon kisan da mazauna garin suka yi wa mai ba su labarin.

An tattaro cewa kwanaki hudu kafin harin, mazauna kauyen sun gano tare da kashe wani mai ba da rahoto wanda ke aiki da ‘yan fashin.

Wata majiya ta shaida Mana cewa maharan wadanda suka zo kan babura, nan da nan suka fara harbe-harbe ba kakkautawa wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 11.

Yanzu Haka mazauna kauyukan na ci gaba da ƙaura, suna barin gidajensu zuwa Dutsin-Ma don neman mafaka.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Katsina, SP Gambo Isa, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Katsina, ya ce mutane uku ne kawai suka mutu ba 11 ba kamar yadda mazauna garin suka ruwaito ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *