
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin‘ yan fashi ne sun kashe sojoji a karamar hukumar Shiroro da ke jihar Neja.
Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun sace mutane sama da 10, sun sace babura bakwai tare da kona motocin sojoji a hare-haren da suka faru a ranar Laraba da safiyar ranar Alhamis.
Garuruwan da ‘yan ta’addan suka kai harin sun hada da Allawa, Manta, Gurmana, Bassa da Kokki a karamar hukumar Shiroro.
Majiyarmu ta gano cewa ’yan bindigar sun kutsa cikin sansanin jami’an tsaro na hadin gwiwa wadanda suka hada da sojoji da’ yan sanda da jami’an tsaro na farin kaya da ’yan banga a Allawa suka bude musu wuta.
An kuma kashe wani jami’in hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) a yayin da jami’an tsaro da dama suka samu raunuka.
Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun kai hari kauyukan Manta, Gurmana da Bassa a ranar Laraba, inda suka kashe wani Alhaji Sale a yankin Madalla sannan suka yi awon gaba da mutane hudu.
Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban kungiyar Shiroro Youth Movement, Mohammed Sani Idris, ya ce barayin da yawansu ya kai 100, suna dauke da bindiga kirar AK47.
Ya ce sun kai hari kan al’ummomin na kimanin awanni biyar ba tare da kalubalantar su ba.
“A yayin mamayar, sun kashe wani Alhaji Sale a garin Madalla da ke karkashin yankin Bassa sannan suka yi awon gaba da mutane hudu suka tafi da babura biyu”
“Har ila yau, a Kokki Boddo wani gari da ke karkashin gundumar Gurmana, sun sace mutum shida kuma sun tafi da babura biyar, an kuma yi garkuwa da mutane biyar a yankin Manta,” in ji shi.
Idris ya yi kira ga gwamnatocin tarayya da na jihohi da su rubanya kokarinsu na ceto rayukan mutane a cikin al’ummomi daban-daban.
Kokarin jin ta bakin ‘yan sanda game da lamarin ya ci tura saboda jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Wasiu Abiodun, bai amsa kiran waya ba kuma bai amsa sakonnin da aka aika masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.