Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Saki Dalibai 27 Na Kwalejin Noma Dake Kaduna

Dalibai 27 na Kwalejin Noma da Ilimin Gandun Daji ta Tarayya, Afaka, jihar Kaduna an sake su.

Daya daga cikin mutanen da suka karbi daliban ya tabbatar wa Daily Trust labarin.

Ya ce kwamitin tattaunawa na Sheikh Abubakar Gumi ne ya taimaka wajen sakin tare da goyon baya daga tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Daliban na daga cikin mutane 37 da aka sace kusan watanni biyu da suka gabata.

Bayan biyan kudin fansa daga iyaye da shugabannin makarantar, ‘yan bindigan sun saki 10 kawai daga cikin wadanda aka yi garkuwar da su.

Tun da farko wadanda suka sace su sun nemi Gwamnatin Jihar Kaduna ta ba su kudin fansa har Naira miliyan 500 amma Gwamna Nasir El-Rufai ya yi watsi da batun tattaunawar, yana mai cewa ‘yan bindiga sun cancanci a kashe su.

Karin bayani nan gaba…

Daga ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *