Da dumi dumi ‘yan ta’adda sun sake kashe mutun biyu daga cikin Daliban da Suka sace a jami’ar Jihar kaduna.

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kisan wasu karin daliban jami’ar Greenfield biyu da ‘yan bindiga suka sace,‘ yan kwanaki bayan kashe wasu uku.

Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ayau ranar Litinin.
A cewar kwamishinan, hukumomin tsaro sun sake gano gawarwakin wasu daliban biyu a yayin aikin ceton daliban
Mista Aruwan ya kara da cewa an kwashe gawarwakin da aka kwaso zuwa dakin ijiye gawarwaki, kuma an sanar da jami’ar game da ci gaban.

Sanarwar ta lura cewa, “Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasir El-Rufai ta yi bakin ciki da wannan mugunta da aka aikata a kan daliban da ba su ji ba ba su gani ba wadanda aka sace yayin da suke ci gaba da neman iliminsu don samun kyakkyawar makoma.”

“Gwamnati na mika sakon tausayawa ga danginsu da shugabannin jami’ar, tare da yin addu’ar Allah ya jikan su.

“Gwamnati za ta sabunta ‘yan kasar kan ci gaban abubuwan da ke faruwa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *