Da dumi dumi ‘yan ta’adda sun saki dabilan da Suka sace a jami’ar Jihar kaduna.

Labarin da muke samu yanzu Cewa Yan makaranta 27 da Yan fashi suka sace daga Kwalejin Koyon Gandun Daji ta Tarayya, Afaka, jihar Kaduna, an sake su.

Daya daga cikin mutanen da suka karbi daliban ya tabbatar Mana da labarin.

Ya ce kwamitin tattaunawa na Sheikh Abubakar Gumi ne ya taimaka wajen sakin tare da goyon baya daga tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Daliban na daga cikin mutane 37 da aka sace kusan watanni biyu da suka gabata.

Bayan biyan kudin fansa daga iyaye da shugabannin makarantar, ‘yan fashin sun saki 10 kawai daga cikin wadanda aka yi garkuwar da su.

Tun da farko wadanda suka sace su sun nemi Gwamnatin Jihar Kaduna ta ba su kudin fansa har Naira miliyan 500 amma Gwamna Nasir El-Rufai ya yi watsi da zabin tattaunawar, yana mai cewa ‘yan ta’addan sun cancanci a kashe su ba a Basu kudin fansa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *