Labarai
Da Dumi Dumi:Dan majalisar dokokin jihar Legas ya rasu bayan ya halarci yakin neman zaben Tinubu a garin Jos

Shugaban kwamitin majalisar dokokin jihar Legas mai kula da ayyukan kananan hukumomi, Sobur Olawale aka Omititi, ya rasu.
Dan majalisar wanda ke wakiltar mazabar Mushin ll a majalisar, ya rasu ne bayan ya halarci yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a garin Jos na jihar Filato.
Olawale ya fadi ya mutu a filin wasa na Rawang Pam Township da ke Jos, wurin da aka gudanar da taron.
Sai dai ba a gano musabbabin mutuwarsa ba, kamar yadda Ripples Nigeria ta rawaito.