DA DUMI-DUMIN SA! Kasar Isra’ila ta kashe manyan Likitoci biyu Palasdiwa masu aikin ceton rayukkan al’umma

Kasar Isra’ila ta kashe manyan Likitoci biyu Palasdiwa masu aikin ceton rayukkan al’umma

Yanzu-yanzu an tabbatar da mutuwar Dakta Mooein Ahmad al-Aloul da kuma Dakta Ayman Abu al-Ouf wadanda su ke shahararrun Likitoci ne a kasar Palastine.

Ayman Abu al-Ouf shine shugaba mai kala da fannin magunguna a babbar Asibitin Al-Shifa, kuma an kashe shi ne tare da iyalansa da ‘yan uwan sa.

Haka shi ma Dakta Mooein Ahmad al-Aloul babban Likiti ne wanda aka tabbatar cewa tun sanda aka fara wannan rikici yake aikin ceton rayukkan al’umma a Gaza.

An dai hallaka su ne da sanyin safiyar yau Litinin ne a lokacin da Isra’ila ta harbo wata roka zuwa Asibitin da su ke aiki.

Ubangiji Allah ya jikan su da rahama.

Daga: Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *