Da Dumi Duminsa: An Kama Wasu Mutane Masu Tono Gawarwakin Jarirai A Kaduna

A Yau a cikin daren nan akayi Nasarar Kama wasu mutane guda biyu Sunje makabarta dake Sabon garin Nasarawa dake jahar Kaduna Sun ciro gawarwakin Jarirai Guda biyu Suka sashi a cikin buhu.

Ankama mutanen ne bayan Sallar isha’i Yan Kato da gora sun kamasu Suka kaisu ofishinsu domin suji tabbacin abinda ya Faru Amma saidai matasan anguwa basu yarda da kulle su da akayi ba sukace Dole sai an Basu mutanen Nan sundauki doka a hannunsu Amma Yan Kato da Goran wato Civilian J.T.F sun hana.

A Haka sukaga abin yana neman fin karfin su shinefa Nan take suka Kira jami’an tsaro domin su tafi dasu, anan fa matasan anguwa sukataso Suka ce Basu yarda ba gardama ta kaure tsakaninsu da jami’an tsaro nanfa jami’an tsaro suka fisataa Suka fara watsa tear gas tare dayin harbi Nan kowa ya watse sannan Suka samu Suka tafi da mutanen domin Yi musu hukunci .

Allah ubangiji muke roko ya tsaremana imaninmu ya karemu da aikaata aikin Ashha yarage Mana son Duniya

Mikiya

Daga: Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *