Da Dumi-Duminsa: Dakarun Soji Sun Kashe ‘Yan Ta’addan Boko Haram Guda 10

‘Yan sa’oi kadan bayan da aka nada sabon shugaban hafsan sojan kasar (COAS) Manjo Janar Faruk Yahaya ya fara aiki, sojojin na Najeriya sun dakile wani hari da’ yan ta’addan Boko Haram suka kai musu a Rann, jihar Borno, inda suka kashe 10 daga cikin ‘yan ta’addar a yayin gudanar da aikin.

A cewar wata sanarwa da kakakin rundunar, Birgediya Janar, Mohammed Yerima, ya sanya wa hannu a ranar Asabar, ‘yan ta’addan sun zo ne da yawansu dauke da manyan bindigogi kuma suka yi yunkurin kutsawa cikin babbar kofar shiga garin.

Ya ce, sojojin, duk da haka, “sun fatattaki ‘yan ta’addan da suka dawo tare da tabbatar da cewa babu sauran wata barazana ga garin da mazaunanta.”

Yerima ya kara da cewa “Sojojin da ke da karfin gwiwa sun kasance a shirye don dakile wannan yunkuri kuma sun yi mummunan rauni a kan ‘yan ta’addan da suka yi watsi da mummunan aikinsu kuma suka kai ga gaci.”

Bugu da kari, sojojin sun yi nasarar lalata daya daga cikin motocin bindigogin kuma sun kwato makamai da dama da suka hada da bindiga ta kakkabo jirgin sama, da kananan bindigogi biyu, da bindigogin AK-47 guda takwas.

Sabon COAS, Faruk Yahaya, a ranar Juma’a ya fara aiki a hedkwatar rundunar da ke Abuja.

Shugaba Muhammad Buhari ne ya nada shi a ranar Alhamis, inda ya zama Babban Hafsan Soji na 22 a kasar.

Ya maye gurbin Ibrahim Attahiru, wani Laftanar Janar, wanda ya mutu a hatsarin jirgin sama a makon da ya gabata.

Har zuwa lokacin nadin nasa, sabon hafsan sojojin ya kasance kwamanda na Operation Hadin Kai, aikin yaki da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *