Da Dumi-Duminsa: Kungiyar Kwadago ta ba Gwamna El-Rufai awanni 48 ya dawo da wadanda aka kora daga aiki

Rikicin masana’antu a jihar Kaduna ya ci gaba yayin da Kungiyar Likitoci da Ma’aikatan Lafiya ta Najeriya (MHWUN) ta ba wa gwamna Nasir El-Rufai wa’adin awanni 48, inda ta umarce shi da ya dawo da ma’aikatan jinya da aka kora wadanda ke kasa da mataki na 14.

Gwamnan na Kaduna ya ba da umarnin korar wasu ma’aikatan jinya da ba su je aiki ba ko kuma suka shiga yajin aikin gargadi na kungiyar kwadagon Najeriya (NLC) a jihar.

Sai dai kuma, kungiyar ta MHWUN a cikin wata sanarwa daga shugaban ta, Biobelemoye Joy Josiah, ta soki gwamnan kan korar ma’aikatan lafiyar, Daily Trust ta ruwaito.

Kungiyar kwadagon ta ce baya ga dawo da ma’aikatan jinyan da aka kora, ya kamata El-Rufai ya nemi gafarar ma’aikatan Najeriya kan abubuwan da ya yi.

Kungiyar ta yi nuni da cewa korar ma’aikatan jinyar karya dokar kasa ne kuma rana ce ta bakin ciki ga dimokiradiyya.

MHWUN ta bayyana cewa zata iya ɗaukar mataki tare da haɗin kan korarrun ma’aikatan.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *