Da Dumi-Duminsa: Rundunar Ƴan sandan Jihar Katsina Tayi Babban kamun Wani ƙasurgumin Barawo

Mai Magana da yawun Rundunar Ƴansandan Jihar Katsina SP Isah Gambo ne ya bayyana kama Wani Matashi da ya ƙware wajen haura gidajen Mutane tareda yi masu Sata, Matashin dai an kamashi da laifin shiga wani Gida ya Fasa Mota tareda sace wayoyin salula guda Ɗari Biyu da Saba’in da Ukku wadanda kudin su ya kama Naira Milyan Goma Sha Biyar (N15,000, 000;00K)

A ranar 22/04/2021 da misalin 07:00hrs, bisa rahotannib sirri rundunar ƴansandan da Damƙe wani Ibrahim Lawal, wanda akafi sani da ‘ABBA KALA’, Dan Kimanin Shekaru Ashirin da Ukku 23 dake Unguwar Fegi a ƙaramar hukumar Daura ta jihar Katsina, barawon wanda dama ansha kamashi da laifukan da sukayi sanadiyyar zuwan shi gidan waƙafi, ya shahara wajen fasa gidajen Mutane tareda yin sata ta kaya dama Babura.

Rana ta baci ne ga wannan barawon lokacin da ya kutsa kai Gidan wani Kamalu Ibrahim, Dan Kimanin Shekaru Talatin da Ukku 33 dake Unguwar Shagari Low cost, Daura, ya fasa mashi Mota ƙirar, BMW 3 Series, da take da registration number kama haka: JW 01 DRA Inda yayi awon gaba da wayoyin salula guda Ɗari Biyu da Saba’in da Ukku wadanda kudin su ya kama Naira Milyan Goma Sha Biyar (N15,000, 000;00K) yayi gudanar da bincike an samu dukkanin wayoyin da ya sace a wurinshi, kuma ya amsa laifin shi.

Rundunar Ƴan sandan ta bayyana cewa zata gurfanar dashi a gaban ƙuliya da zarar ta kammala binciken ta.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *