Da Dumi-Duminsa: Saura kwana 5 kacal mu rufe layukkan da ba a hada da NIN ba~ Pantami

Saura kwana 5 kacal mu rufe layukkan da ba a hada da NIN ba, Cewar Sheikh Ali Isah Pantami

Wa’adin da hukumar da ke kula da harkokin sadarwa ta Najeriya karkashin jagorancin Minista Pantami wato NCC ta ɗiba domin yin rajistar layin waya da lambar shaidar zama ɗan ƙasa ta NIN saura kwana 5 kacal ya kare.

NCC ta tunatar da ƴan Najeriya a shafinta na Twitter cewa ranar shida ga watan Mayu wa’adin da ta bayar zai cika.

Don haka hukumar ta bayyana cewa nan da kwana 5 duk layin wayar da ba a yi wa rajista ba da lambar NIN za a rufe shi nan take.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *