Da Dumi Dumi’yan Bindiga sun sake Kai Hari hukumar zabe INEC.

Rundunar ‘yan sanda a jihar Anambra ta tabbatar da kai hare-hare a hedikwatar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta da‘ B’Division na ‘yan Sanda a Awka, babban birnin jihar a daren Lahadi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda na jihar, Ikenga Tochukwu, ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai ya ce yanzu yana da karancin sani kan lamarin.

Ya ce, “Don Allah ku Dan jira zan dawo gare ku da zarar na samu cikakken bayani.”

Wasu ‘yan bindiga da kimanin karfe 9 na daren ranar Lahadi suka mamaye ofishin na B Division da kuma ofishin hukumar zabe INEC da ke Awka.

Kawo yanzu dai ana zargin Cewa wasu jami’an ‘yan sanda ana fargabar sun mutu a harin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *