Da dumi’dumi: A kan Hanyar su ta komawa gida daga taron Apc a Kano mutun bakwai sun yi hadarin mota sun mutu nan take.

Tsohon kwamishinan Ilimi na jihar Kano Kuma Dan takarar Neman zama Dan majalisar wakilai Mai wakiltar Kiru da bebeji Hon Sanusi majidadi kiru ya bayyana rasuwar mutanen bakwai a shafin sa na Facebook Yana Mai cewa.
Innalillahi Wa’inna Ilaihil Rajiun !!!
Mutane shida ne daga mazabar Yalwa, Kwanar Dangora suka rasu sakamakon mummunan hadarin mota da sukayi akan komawarsu gida daga taron mu na yau din nan na Jamiyyar Apc.
Na cikon bakwai din shima ya rasu yanzun nan bayan isowarsu asibitin Murtala dake Jihar Kano bayan mun gana da babban likita ya tabbatar mana da rasuwarsa.
Kamar yadda Jagoran tafiyarmu ta APC Alhaji Abubakat Mai – Mai ya tabbatar mutane uku daga Unguwar Diraman, daya daga gidan Algaita sannan uku daga garin Kariya.
A madadina, iyalina da dukkanin al’ummar wannan Karamar Hukuma tamu ta Kiru, ina mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadannan bayin Allah da fatan Allah ya kai rahama kabarinsu ameen.
Anyi jana’izarsu a yau da safen nan kamar yadda addinin Islama ya tanada manyan jam’iyar Apc na yankin sun sami halartar jana’izar wanda suka ha’da da
Ahaji Abubakar Me Mai
Senator Kabiru Ibrahim Gaya
Sanusi Muhammad majidadi kiru
Hon. Kabiru Hassan Dashi
Hon Muntari Isyaku Kmaiyaki
Sani Kanti Ranka da dai sauran manyan baki.
Kawo yanzu uwar Jam’iya ta Kasa batayi ta’aziyyar wa’yanda suka rasa sansu ba.