Labarai

Da ‘dumi’dumi: ASUU Jingine Yajin Aiki Tayi ba wai ta kawo karshen Yajin Aikin bane babu maganar komawar dalibai makaranta sai an cika sharadi.

Spread the love

Bayan kwashe kusan watanni takwas, kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) a safiyar ranar Juma’a ta dakatar tare da jinginr yajin aikin da ta shiga “bisa sharadi. “

Kungiyar ta dauki matakin ne a karshen taron da ta kammala a safiyar yau a Sakatariyar ta ta kasa da ke Jami’ar Abuja.

Wani shugaban ASUU ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

ASUU dai ta jingine Yajin Aikin ne ba tare da Kiran dalibai dasu koma makaranta ba sun Kuma ce a akwai sharadi na zuwa daga baya.

Dakatar da Yajin Aikin tare da Jinginewa ta Biyo bayan hukuncin wata babbar kotun tarayya ne a makon daya gabata na cewa dole ne Malaman su koma makaranta su cigaba da koyarwa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button