A zaman daya gudana a gidan farfesa Jerry Gan An hana ‘yan jarida daukar Hoto.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gana da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike a Abuja ranar Alhamis.
An gudanar da taron ne a bayan fage kuma babu wata jam’iyya da ta tabbatar da gudanar da taron a hukumance.
Sai dai wata majiya mai tushe ta shaida wa gidan talabijin na Channels cewa sun gana ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kokarin sasanta rikicin da ke tsakanin jam’iyyar PDP.
Rahotanni sun ce ganawar ta gudana ne a gidan Farfesa Jerry Gana, mamba a kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP.
A ranar Laraba ne dai kwamitin PDP ya yanke shawarar sasanta bangarorin biyu gabanin babban zaben 2023.
Ana sa ran Wike zai marawa Atiku baya a zaben 2023 amma alamu sun nuna cewa gwamnan jihar Ribas bai ji dadi ba bayan an ba shi tikitin mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne Wike ya caccaki Atiku Abubakar kan karyar da ya yi masa, duk da cewa ya sha alwashin ci gaba da zama a PDP.
Atiku ya yi alkawarin hada kan jam’iyyar gabanin zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa.