
Dan majalissar tarayya mai ci a yanzu Hon. Rimamde Shawulu mai wakiltar kananan hukumomin yankunan Donga/Takun/Ussa da Yangtu dake jihar Taraba Hon Rimamde Shawulu ya fice daga Jam’iyyar PDP ya koma jam’iyar NNPP ta Sanata Rabi’u Musa kwankwaso Mai kayan marmari.
A tare da dan majalisar akwai zababben Dan majalissar jiha mai ci a yanzu Hon. Nasir Tafida tare da tsohon minister kuma tsohon Sanata Hon. Joel Ekenya dukkanin su sun canja sheka zuwa jam’iyyar NNPP mai kayan marmari bisa jagorancin Alh Umar Adamu Sarki.
jam’iyar NNPP na cigaba da kwashewa jam’iyar APC da PDP jiga-jigan Siyasa wanda suka hada da Sanatoci Yan majalisu tare da tsofaffin gwamnoni.