Labarai

Da ‘dumi’dumi: Gobe ne Kwankwaso zai fitar da manufofin sa da Kuma kwamitin Yakin neman zaben sa na 2023.

Spread the love

A gobe Talata ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP), Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso zai gabatar da Kudirin manufofin yakin neman zabensa.

Jaridar SAHELIAN TIMES ta tattaro cewa za a fitar da Kudrin tare da tsarin kamfen din na shugaban kasa ne kwana guda bayan wani taron kololuwa da aka shirya na bikin cikarsa shekaru 66 a Abuja.

A baya dan takarar shugaban kasar ya yi ikirarin cewa jam’iyyar ce ta fi dacewa.

Ya bukaci ‘yan Najeriya da su rika ganin NNPP a matsayin mai ceton su.

Sanata Kwankwaso ya dage cewa jam’iyyar ita ce mafi alheri ga Najeriya, inda ya bukaci masu kada kuri’a da su tabbatar sun fito baki daya don amfani da ‘yancinsu a zaben na 2023.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button