Labarai

Da ‘dumi’dumi: Gwamna masari ya Haramtawa Atiku taron Gangamin Yakin Neman Zaben sa a Filin Wasa Na Karkanda dake jihar katsina.

Spread the love

Gwamnatin jihar Katsina ta hana PDP filin wasa na Karkanda domin yin taron zuwan Atiku Abubakar

Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta hana jam’iyyar PDP yin anfani da filin wasa na Muhammadu Dikko wanda aka fi sani da Karkanda domin yin taron gangamin yakin neman zaben Alhaji Atiku Abubakar saboda wasu gyare-gyaren da ake yi a filin wasan. 

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata takardar da Ibrahim Nuruddeen ya sa ma hannu a madadin Sakataren Gwamnatin jihar Katsina mai dauke da kwanan wata na 13 ga watan Disemba da Katsina Post ta samu. 

A takarar dai, gwamnatin jihar ta nanata cewa tana

aikin gyaran filin wasan ne don haka ba zata iya bada shi ba ga jam’iyyar kamar yadda ta shaida a baya. 

Tuni dai jam’iyyar ta PDP ta sauya wurin yin gangamin taron na Atiku Abubakar zuwa filin wasan dawaki watau filin Polo. 

Ana sa ran zuwan dan takarar shugabancin kasar Najeriya Na jam’iyyar ta PDP ne a jihar ta Katsina ranar Talata mai zuwa 20 ga watan Disemba, 2022. 

A shekarar 2015 ma dai gwamnatin Barista Ibrahim Shema ta hana jam’iyyar APC da dan takarar ta na Shugaban kasa a wancan lokacin, Janar Muhammadu Buhari yin anfani da filin wasan na Karkanda domin yin gangamin yakin neman zaben su. 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button