Labarai

Da ‘dumi’dumi: Gwamnan jihar Oyo na jam’iyar PDP yace su Yarabawa duk Tinubu zasu zaba a zaben shugaban kasa na 2023.

Spread the love

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde a ranar Lahadi ya aike da sakon hadin kai ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu a zaben 2023.

Mataimakin gwamnan jihar Oyo, Bayo Lawal wanda ya wakilci Seyi Makinde a jihar Ondo ne ya bayyana hakan a wajen liyafar da jagoran kungiyar Afenifere, Pa Reuben Fasoranti ya yi wa Tinubu.

Ku tuna a baya Vanguard ta ruwaito cewa Tinubu zai ziyarci Fasoranti da kuma shugabannin kungiyar Afenifere, kungiyar al’adu da siyasa ta Yarbawa domin gabatar da shirinsa na Action Plan kan yadda yake da niyyar tinkarar matsalolin tattalin arziki da sauran matsalolin da kasar nan ke fama da su.

Seyi Makinde da wasu gwamnonin PDP hudu da ake kyautata zaton sun fusata kan rikicin shugabancin jam’iyyar sun yi takun-saka da shugaban jam’iyyar PDP, Sanata Iyorcha Ayu kan batun shiyyar kujerar shugaban jam’iyyar.

Makinde kuma, gwamnan jihar Ribas, Nyesome Wike, ya kauracewa taron kaddamar da yakin neman zaben Atiku a jihar Akwa Ibom ciki har da yakin neman zaben da aka gudanar a jihar Edo, matakin da ake kyautata zaton ya kara tayar da zaune tsaye a sansanonin magoya bayan Atiku.

Masana harkokin siyasa sun yi hasashen sauya sheka inda wasu da dama ke ganin gwamnonin PDP biyar da suka fusata ciki har da Makinde na iya kafa tantunan su tare da dan takarar shugaban kasa na APC, Tinubu.

Da yake magana cikin harshen Yarbanci a wajen taron, mataimakin gwamnan jihar Oyo, Mista Bayo Lawal wanda ya wakilci Gov Makinde, ya jaddada cewa al’ummar jiharsa za su tsaya tare da shawarar shugabannin Yarbawa dangane da zaben shugaban kasa na 2023.

Kalamansa: “Tun da Makinde ya zama gwamna, ba ya wasa da duk wani abu da ya shafi Yarabawa, duk lokacin da baba (Pa Fasoranti) ya kira shi, a ko da yaushe yana nan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button