Labarai

Da ‘dumi’dumi: Kotun Amurka ta yankewa Hushpuppi hukuncin daurin shekaru Sha daya 11, ta umarce shi da ya biya $1.7m ga wadanda abin ya shafa.

Spread the love

Hushpuppi ya amsa laifinsa a watan Afrilun 2021 kan tuhumarsa da hada baki da safarar kudade, watanni 10 bayan kama shi a Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), a watan Yuni 2020.Bayan dage zaman da aka yi na tsawon watanni, wata kotun Amurka a Los Angeles, California, a ranar Litinin, ta yanke wa dan damfara na kasa da kasa, Ramon Olorunwa Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi hukuncin daurin sama da watanni 135 – sama da shekaru 11 – a gidan yari na tarayya.Alkalin na Amurka Otis D. Wright II ya umarci mai laifin mai shekaru 40 da ya biya dalar Amurka $1,732,841 diyya ga wasu mutane biyu da aka damfara, kamar yadda wata sanarwa da kotun ta aike wa gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.Alkalin ya ce Hushpuppi ya hada baki ne wajen karkatar da dubban miliyoyin daloli ta hanyar zamba ta yanar gizo tare da bayyana irin salon rayuwar sa na jin dadi da samun kudade a shafukan sada zumunta.Ya amsa laifinsa a watan Afrilun 2021 a kan tuhume-tuhume guda daya na hada baki da safarar kudade, watanni 10 bayan kama shi a Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), a watan Yuni 2020.Hushpuppi ya ci gaba da kasancewa a hannun gwamnatin tarayyar amarka tun bayan korar sa daga Hadaddiyar Daular Larabawa.Lauyan Amurka Martin Estrada ya ce “Abbas ya yi alfahari a shafukan sada zumunta game da salon rayuwar sa – salon da ya samu ta hanyar sa hannun sa a zamba da kuma hada-hadar kudi da ake yi wa wadanda abin ya shafa a duniya.””Samun kudaden haram da zamba na imel na kasuwanci babbar matsalar laifuka ce ta kasa da kasa, kuma za mu ci gaba da yin aiki tare da jami’an tsaro da abokan hulda na kasa da kasa don ganowa da gurfanar da wadanda ke da hannu a gaban kotu, a duk inda suke.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button