Labarai

Da ‘dumi’dumi: kungiyar Alhuqqu zata daukaka Kara Kan hukuncin Sheikh Abduljabbar zuwa babbar kotun tarayya.

Spread the love

Kungiyar Alhaqqu Human Rights and Social Justice Organisation ta ce ta kammala shirin daukaka karar hukuncin kisa ta hanyar rataya da aka yanke wa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara mai shekaru 52.

Majiyarmu ta DCL Hausa tacr Solace Base ta ruwaito shugaban kungiyar Sa’id Bn Usman na cewa ba su gamsu da shari’ar da aka yi wa malamin da aka samu da laifin yin batanci ga addinin Islama ba, yana mai cewa hakan ta sa kungiyarsu ta tuntubi iyalan malamin kuma sun yanke shawarar daukaka hukuncin kotun.

Da ma dai Alkali Ibrahim Sarki Yola da ya yanke hukuncin kisan ga malamin a ranar Alhamis ya ce Abduljabbar mai bin darikar Qadiriyya zai iya daukaka kara a cikin kwanaki 30. Sai dai tun a cikin kotun malamin ya bukaci a yi gaggawar kashe shi domin a cewarsa zai yi mutuwa ta girma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button