Labarai

Da ‘dumi’dumi: kungiyar Tijjaniyya a Kaduna ta bayyana goyon bayanta ga Sanata Uba sani.

Spread the love

Sanata Uba sani Dan takarar Gwamnan jihar Kaduna karkashin jam’iyar APC ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter Yana cewa nayi matukar Jin dadi sakamakon amincewar da na samu daga muhimmiyar kungiya ta addini wato Tijjaniyya Grassroots Mobilisation and Empowerment Initiative of Nigeria (TIGMEIN).

A wani taro da na yi da kungiyar, na tabbatar musu da kudiri na na gudanar da gwamnati mai gaskiya da rikon amana idan aka zabe ni a matsayin Gwamnan Jihar Kaduna a 2023.

A matsayina na Mai kare haƙƙin ɗan adam na tsawon lokaci ni kaina, na fahimta kuma na yaba da gagarumar gudunmawa da sadaukarwar da ƙungiyar ta bayar don ƙarfafa jama’a da tabbatar da al’umma ta gari. Ina yaba musu bisa ga ayyuka masu kima ga marasa galihu, marasa aikin yi da marasa murya Mai tsayi.

Domin kara musu kwarin guiwa da kuma kara inganta ayyukansu, na bayar da gudummawar motar bas ga kungiyar tare da tabbatar musu da cikakken goyon bayana a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

A karshe na yaba da irin goyon bayan da suke ba su, sannan na bukace su da su zabi dan takararmu na shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da sauran ‘yan takarar jam’iyyar APC a dukkan matakai a zabe mai zuwa.

Sanata Uba sani na Cigaba da samun karbuwa daga al’ummar jihar Kaduna.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button