Labarai

Da ‘dumi’dumi Kwankwaso ya nada kwamitin mutun hudu domin zuwa cika sharu’dan Doguwa na ta’aziyyar rasuwar mahaifinsa.

Spread the love

Sanata Rabi’u musa Kwankwaso ya kafa kwamiti domin dawo da shugaban masu rinye na majalisar wakilan Nageriya Hon Alhassan Ado doguwa zuwa ga jami’iyyar NNPP Kamar yadda Mataimakin sa na harkokin sada zumintar zamani Ibrahim Adam ya bayyana Yana Mai cewa da Jin Da’awar hon Doguwa Jagoranmu (Sen. Kwankwaso) ya kafa wani babban kwamiti mai wakilai mutun 4 don ziyarar ta’aziyyar Doguwa karkashin jagorancin Sen. Rufa’i Sani Hanga tare da (Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum da Shugaban jam’iyyar mu, Hon. Umar Haruna Doguwa da Hon. Sarki Aliyu Daneji a matsayin mambobin tawagar.”

Rt. Hon. Rurum ya tabbatar da cewa za su kai ziyarar ta’aziyyar ne a madadin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP H.E Rabiu Musa Kwankwaso da wuri domin cika sharuddan dan uwanmu Hon. Alhassan Ado Doguwa da kuma tabbatar da cewa manyan kifi na cikin gidan yanar mu nan bada jimawa ba.

“Ina magana ne da amincewar Sen. Rabi’u Musa Kwankwaso kuma a madadin kwamitin maza 4, a siyasance, ba aboki na dindindin, haka ma ba makiya na dindindin, amma muna son inganta zumunci ba abokan gaba ba.” Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum ya nanata”. batun.

a makon Nan ne dai hon Alhassan Ado doguwa yace idan Kwankwaso ya turo tawaga sukayi Masa ta’aziyya rasuwar mahaifinsa ko Kuma ya kirashi a waya to tabbas zai koma tafiyar sa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button