Labarai

Da dumi’dumi: Mu Bamu kama gwamnan bankin Nageriya ba Kuma Bamu da Shirin kamashi ~Cewar DSS.

Spread the love

Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele a yau ranar Litinin ya koma bakin aiki bayan hutun da ya yi a kasar waje.

Daraktan Sadarwa na CBN, Osita Nwanisobi ne ya bayyana haka a wata sanarwa.

Sanarwar ta kara da cewa, “Gwamnan babban bankin ya koma aiki tare da sabunta kwarin guiwa don gudanar da aikinsa gabanin taron kwamitin kula da harkokin kudi na farko (MPC) na shekarar da aka shirya gudanarwa a ranar 23 zuwa 24 ga watan Janairu, 2023,” in ji sanarwar.

Emefiele ya ci gaba da jajircewa wajen gudanar da aikin da ke gabansa kamar yadda rantsuwar kama aiki da kuma tsarin manufofin shugaban kasa Muhammadu Buhari.”

Haka Kuma hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) a yau ranar Litinin din nan ta ce jami’anta ba su “ mamaye ofishin CBN ba don kama gwamnan babban bankin ba.

“An jawo hankalin hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) kan labarin karya da ake yadawa cewa jami’anta sun mamaye babban bankin Najeriya tare da kama gwamnan, a yau 16/1/23. Wannan labari ne na karya kuma yaudara ce,” in ji kakakin DSS, Peter Afunanya a cikin wata sanarwa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button