Labarai

Da ‘dumi’dumi: Muna zargin wasu Gwamnonin Arewa da wata boyayyar manufar Shirin zaben Kwankwaso a zaben 2023 ~Cewar na hannun damar Bola Tinubu.

Spread the love

Wasu jigogin jam’iyar APC a jihar Borno da Oyo sun bayyana cewa akwai kullalliyar Shirin da Gwamnonin Arewa sukeyi na Shirin zaben Sanata Rabi’u kwankwaso a babban zaben shugaban kasa na 2023 jigogin na kusa da Tinubu Wanda suka bayyana wa majiyarmu amma ya bukaci a boye sunansa ya ce suna sane da shirin wasu Gwamnonin Arewa da sukeyi na Shirin zaben Sanata Rabi’u musa Kwankwaso Dan Arewa amatsayin Shugaban kasar Nageriya na gaba.

Jigon yace wasu Gwamnonin Arewa da adadin yawan su ya Kai bakwai suna da boyayyar manufar zaben Tsohon Gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u a zaben na 2023 yace Yan Arewa suna sane da irin yadda Yan kudancin Nageriya ke kokarin nuna kabilanci da Siyasar yanki da nufin Raba Kan Al’ummar Nageriya dukda sunsan Yan arewa ne ke da jama’ar da zasu iya zaben Wanda suke so domin Zama shugaban kasa.

Sanata Rabi’u musa Kwankwaso Yana daga cikin ‘yan takara hu’du da ake zaton suna da damar cin zaben na 2023 sauran Yan takarar sun ha’da da Bola Tinubu Atiku Abubakar da Kuma Peter Obi.

Kawo yanzu ba a bayyana sunan Gwamnonin dake da wannan Shirin ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button