Labarai

Da ‘dumi’dumi: Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta karyata batun sace kwamishinan ‘yan sandan jihar Wanda muka wallafa a makon daya Gabata Cp Ari Mohammed Ali 

Spread the love

Rundunar ‘yan sanda jihar Delta sun karya ta labarin cewa an sace kwamishinan ‘yan sandan jihar Cp Ari Mohammed Ali idan dai za’iya tunawa a ranar talatar data gabata ne Mikiya ta wallafa labarin cewa an sace kwamishinan ‘yan sandan ne a Lokacin daya Kai ziyara Lafia babban Birnin Jihar sa ta haihuwa wato Nasarawa Bayan fitar labarin ne kakakin ‘Yan Sandan Jihar Nasarawa ya sanar damu cewa wannan labarin bai tabbata ba Babu batun sace kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Delta domin a jihar Nasarawa ma Babu da labarin Mai Kama da wannan.

Haka Kuma bayan Fitar labarin rundunar ‘yan sandan jihar ta Delta itama ta tabbatar Mana da cewa Cp Ari Mohammed Ali na Ofishin sa Yana gudanar da Ayyukan sa na yau da kullum a Lokacin da wannan labari ya fita.

Da hakane muke cewa a madadin Sashin gudanarwa na Gidan wannan jarida Mikiya mallakin Kwamfanin MIKIYA ONLINE NEWS LTD, zamu yi anfani da wannan dama domin Mika sakon Bayarda hakuri da neman gafara bisa fitar da wannan labari Ga kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Delta Cp Ari Mohammed Ali musamman iyalan sa tare da ‘yan Uwa da abokin arziki da Kuma rundunar ‘yan Nageriya karkashin jagorancin IGP Alkali Baba Usman da duk wanda fitar wannan labari ya tayarwa da hankali Muna bayarda hakuri bisa hakan.

Har’ila Bincike ya tabbatar Mana da cewa kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Delta Cp Ari Mohammed Ali Yana daya daga cikin shugabannnin ‘yan sanda mafi kwazo da kokari da hazaka da gudanar da Ayyukan bisa gaskiya da amana duk  a kokarin sa na ganin kasa ta samu tsaro Mai ingancin zuwa matakin zaman lafiya hakan ne ma yasa ya samu tarin Lambobin Yabo kala kala daga kungiyoyi da dama.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button