Labarai

Da ‘dumi’dumi: Sanata Uba Sani ya Tallafawa da Cibiyar Gina gidauniyar Tallafawa Marayu ta Shehu Ibrahim Inyass da Milyan Ashirin 20m.

Spread the love

An karrama dan takarar gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani a kungiyar Fityanul Islam ta Kasa a wani taro da ta shirya a ranar Alhamis.

Dan takarar gwamnan jihar Kaduna na jam’iyyar APC Sanatan Kaduna ta tsakiya Sanata Uba Sani a wajen taron ya bayar da tallafin gina katafaren gidan marayu da koyar da sana’o’in hannu na sheikh Inyass.

An gudamar da taron ne a karkashin jagorancin dan uwansa dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC Samata Kashim Shattima.

Da yake yi wa jaridar Dimokuradiyya karin bayani Uba Sani ya ce ayyukan cibiyar na samar da sana’o’i ta sheikha Ibrahim Inyass ayyuka ne masu muhimmanci guda biyu da idan aka kammala su kuma suka fara aiki, za su shafi rayuwar marasa galihu musamman marayu.

Ya ce “Bukatun marayu na yau da kullum ba kawau za a kula da su ba ne, za a baiwa marayun basirar da za su dogara da kansu,”

“Ta yin haka ne za su zama al’umma masu fa’ida kuma da lokaci ya yi za su zama masu daukar ma’aikata“, inji shi.

Sanata Uba Sani ya ce domin taimakawa wajen aiwatar da wannan aiki da ke kula da marasa galihu da marayu a cikin al’ummarmu, musamman marayu na bayar da gudunmawar Naira miliyan 20.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button