
Majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) ta amince da siyan motocin aiki, na’urorin tsaro, da na’urorin da za su tallafa wa hukumomin tsaro da ke aiki a babban birnin tarayya Abuja a kan kudi Naira biliyan 1.835.
Da yake bayar da cikakken bayani kan sayan bayan taron FEC a ranar Larabar jiya da ta gabata, Ministan babban birnin tarayya, Mohammed Bello, ya bayyana cewa za a sayo motocin alfarma guda 60 masu dauke da na’urorin sadarwa a kan wannan adadin kuma a kawo su cikin watanni biyu.
Bugu da kari, ministan babban birnin tarayya Abuja ya bayyana cewa majalisar ta amince da samar da na’urorin tsaro da na’urori daban-daban don tallafawa hukumomin tsaro a babban birnin kasar nan kan kudi naira miliyan 847.1.
Kayayyakin biyu sun kai Naira biliyan 2.68.
Hakazalika majalisar ta kuma tabbatar da siyan motocin da kudinsu ya kai Naira biliyan 1.4 ga Jamhuriyar Nijar.
Ministar kudi, kasafi, da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed, ta shaida wa manema labarai cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sayan wanda wani bangare ne na kokarin taimakawa jamhuriyar Nijar wajen bunkasa yaki da rashin tsaro.
Sai dai kuma wannan tabbaci da gwamnatin tarayya ta samu ya haifar da tofin Allah tsine daga ‘yan Najeriya inda da yawa ke zargin matakin.