Labarai

Da ‘dumi’dumi: Wata babbar kotu ta Hana Gwamnatin Ganduje sayar da Asibiti dake jihar ta Kano.

Spread the love

Wata babbar kotun jihar Kano mai lamba 16 da ke zamanta a titin Miller Road karkashin jagorancin mai shari’a Maryam Ahmad Sabo ta hana gwamnatin jihar Kano sayar da asibitin haihuwa da yara a unguwar ‘Yan awaki da ke jihar.

Kimanin mazauna gunguwar Yan awaki 113 ne suka shigar da karar mai kwanan wata 20 ga watan Disamba wanda shugabansu Salisu Ibrahim na Yan awaki K/Wamabai ya rantsar.
Sulaiman Gandu ya roki kotu da ta hana Gwamna Abdullahi Umar Ganduje sayarda asibitin

Sauran wadanda ake kara a karar sun hada da babban lauyan gwamnatin jihar Kano da karamar hukumar karamar hukumar.

Mai shari’a Maryam Ahamd Sabo ta aminta da korafin na mazauna garin ‘Yan awaki tare da hana wanda ake kara na farko sayar da asibitin sannan ta umarci dukkan bangarorin da su ci gaba da kasancewa masu bin umarnin kotu har zuwa lokacin da aka dage sauraron karar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button