Labarai

‘Da ‘dumi’dumi: ‘Yan bindiga sun Sace Shugaban karamar Hukumar keffi dake Jihar Nasarawa sun Kuma kashe Odilinsa nan take.

Spread the love

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban karamar hukumar Keffi ta jihar Nasarawa Hon Muhammad Baba Shehu tare da direbansa.

‘Yan bindigar sun kashe jami’an ‘dan sanda dake kula da shugaban hukumar, Seageant Alhassan Habibu Nasir.

Lamarin ya faru ne a gundumar Gudi ta karamar hukumar Akwanga da misalin karfe 6:30 na yammacin ranar Juma’a a lokacin da shugaban ya nufi Lafia.

An kashe jami’an ‘dan sandan ne yayin artabu da ‘yan bindigar a kokarin sa na kare Mai gidansa Kuma sun harbe shi wanda Nan take ya mutu.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun budewa motarsa ​​wuta ne a lokacin da yake tunkarar Gudi, inda suka kashe Odilinsa suka Kuma yi awon gaba da shi da direban sa.

Garin Gudi shine mahaifar gwamnan Jihar Nasarawa Engr Abdullahi A.A Sule.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Nasarawa, ASP Ramhan Ramhan ya tabbatar da faruwar Al’amarin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button