Labarai
Da ‘dumi’dumi ‘Yan bindiga sun tashi bama-bamai a kan jirgin kasan Kaduna Abuja mai dauke da fasinja kusan mutun dubu daya 1,000.


Wasu ‘yan ta’adda da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun tayar da bama-bamai a titin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna tare da yin nasarar hana shi.
Majiya mai tushe ta tabbatar wa DAILY NIGERIAN harin a daren ranar Litinin, inda ta ce an kai harin ne a wani wuri tsakanin Katari da Rijana.
Daya daga cikin fasinjojin da ya tabbatar da faruwar lamarin a wata wayar tarho ya ce maharan sun kewaye jirgin, inda suka rika harbe-harbe.
A halin yanzu dukkan fasinjojin suna kwance a kasan jirgin. ‘Yan bindigar dai suna harbi kai tsaye. Muna cikin babban hadari,” in ji na
fasinjojin da suka firgita.
Akwai akalla fasinjoji 970 a cikin jirgin, a cewar majiyoyin hukuma da suka saba da aikin jirgin.