Labarai

Da ‘dumi’dumi: ‘Yan majalisa biyu a jihar Gombe sun fice daga Jam’iyar APC sun koma jam’iyar NNPP.

Spread the love

Dan takarar jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a jihar Gombe, Khamisu Mailantarki ya kara samun karfin amatsayin dan takarar gwamna Kuma barazana ga jam’iyyar APC mai mulki a jihar ta Gombe hakan ya faru ne Bayan da Yan majalisar jihar guda biyu suka sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP.

‘Yan Majalisun biyu sun ha’da da Hon Hamza Adamu mai wakiltar Balanga ta Kudu da Hon. Bappah Usman Jurara mai wakiltar Funakaye ta Kudu sun sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP ne bayan ganawa da dan takarar gwamna na jam’iyyar, Hon. Khamisu Ahmed Mailantarki.

Sauyin nasu ya zo ne ‘yan sa’o’i kadan kafin kaddamar da yakin neman zaben 2023 da aka shirya yi ranar Asabar.

Wannan ci gaban ya sanya jam’iyyar NNPP ta zama babbar jam’iyyar adawa a jihar tare da mambobin majalisar dokokin jihar.

Da suke zantawa da Wakilinmu jim kadan bayan sauya shekar nasu, ‘yan majalisar biyu sun ce sun dauki matakin shiga jam’iyar Khamisu Mailantarki ne domin maslahar jihar.

Sun bayyana cewa jiga-jigan ‘yan takara biyu na jam’iyyar APC mai mulki da kuma babbar jam’iyyar adawa ta PDP ba su da halayen jagoranci da ake bukata domin hada kai da ci gaban jihar.

Idan dai za a iya tunawa dai da dama daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulki da na PDP sun koma jam’iyyar NNPP a kwanakin baya.

Wadanda suka sauya sheka sun hada da; Mataimakin Daraktan Sabbin Kafafan Yada Labarai na Kwamitin Gudanar da Kamfen na PDP, Hon. Babale Makera ya sa Jam’iyyar ta kara karfi a matsayin manyan ‘yan adawa a jihar.

‘Yan majalisar APC guda biyu daga Gombe sun koma NNPP, sun kara wa Mailantarki samun damar zama gwamna

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button