Da-duminsa: Boko Haram Sun Kai Sabon Hari A Jihar Yobe

Mazauna Kanamma, hedikwatar karamar Hukumar Yunusari da ke Jihar Yobe, sun gudu daga gidajen su, inda da yawa suka kwana a cikin daji yayin da Boko Haram suka yi wa garin kawanya.

Rahotanni sun bayyana cewar kungiyar ta kai hari garin ne a cikin manyan motoci goma dauke da bindigogi da misalin karfe 6:30 na yamma a ranar Alhamis lamarin da ya sa mazauna garin tserewa zuwa cikin daji da kauyukan da ke makwabtaka da su domin kare lafiya.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a daren ranar Alhamis, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda reshen jihar Yobe, ASP Dungus Abdulkarim, ya ce maharan sun far wa Kanamma ne amma ba a samu cikakken bayani ba.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *