Da Duminsa: Ministan Abuja Ya Hana Zuwa Filin Idi a Bikin Karamar Sallah

Daga cikin kokarin shawo kan barkewar cutar COVID-19, Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Malam Muhammad Bello, ya hana yin sallar idi a babban filin Idi na kasa da ke kan babbar hanyar Umaru Musa Yar’Adua.

A cewar wata sanarwa daga Babban Sakataren yada labarai na Ministan, Mista Anthony Ogunleye, Hukumar Gudanarwar Birnin Tarayya (FCTA), ta dauki matakin ne bayan zaman da Ministan ya jagoranta da Majalisar Limaman Abuja.

Ogunleye ya ce tawagar a karkashin jagorancin Shugabanta, Imam (Dr) Tajudeen M.B Adigun, sun sadu da Bello ne domin tattaunawa kan hanyoyin da za a bi domin gudanar da Sallar Idi domin bikin Eid el-Fitr mai zuwa, Daily Trust ta ruwaito.

“Ana umartar mutane su yi Sallar Idi a harabar masallatan Juma’ar unguwanninsu, a kuma rage yawan masu shiga masallaci zuwa kasa da kashi 50%.

“Wajibi ne kuma mahukunta na addini su kula da shige da ficen masu ibada, su kuma tabbatar da kiyaye matakan kariya na sanya takunkumi, ba da tazara, da kuma wanke hannu.

“Bukukuwan Sallah kuma a takaita su zuwa cikin gidaje, yayin da wuraren shakatawa za su kasance a rufe,” in ji sanarwar.

Ministan ya godewa shugabannin addinin kan hadin kan da suka bayar wajen yakar COVID-19, yana mai jaddada cewa bayan an shiga cikin annoba ta farko da kuma ta biyu da ta haifar da asarar rayuka, ya zama wajibi a hana afkuwar yanayi na uku kamar yadda ake gani a wasu kasashe a fadin duniya.

“A kan wannan da abin da muke da yakini a kai, muna kira ga al’ummar Musulmi da su girmama wannan matsaya ta Gwamnatin FCT ta hanyar yin Sallar Idi a kananan hukumominmu.”

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *