Da duminsa: Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci guda biyu

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Mallam Abubakar Nuhu Fikpo matsayin Dirakta Janar na ma’aikatar samar da aikin yi watau NDE.

Hakazalika Buhari ya nada Kwamred Issa Aremu a matsayin Dirakta Janar da Kwalejin Kwadago na kasa (NILS).

Sakon shugaban kasan na kunshe cikin jawabin da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya saki da yammacin Talata.

“Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Mallam Abubakar Nuhu Fikpo matsayin tabattacen Dirakta Janar na Ma’aikatar samar da aiki NDE,” Shehu yace.

“Gabanin nadinsa, Malam Fikpo ya kasance mukaddashin Diraktan ma’aikatar.”

“Hakazalika shugaba Buhari ya nada Kwamred Issa Aremu matsayin Diraktan Kwalejin Kwadago na kasa (NILS).”

“Wa’adin nadin na shekaru hudu ne fari daga ranar 18 ga Mayu, 2021.”

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *